Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Cutar shawarar jarirai, me ye abin yi?
Ana haihuwar jarirai da cutar shawara wadda ke sauya launin idanunsu da fatarsu, cutar da ke sa wasu iyaye shanya yara a hantsi.
Sai dai likitoci sun ce yin hakan ba shi ne mafita ba, domin idan cutar ta yi kamari tana iya shiga kwakwalwa ta lalata ta.
Inda suka bayar da shawarar cewa, ko da ba a haifi jariri da wadannan alamomi na cutar ba, ya kamata uwa ta dinga dubawa kullum har tsawon wata guda bayan haihuwa.
Sannan da zarar ta ga wata alama, ya kamata ta garzaya da jariri zuwa asibiti.
Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce cutar shawarar wadda ake kira Jaundice da turancin ingilishi, cuta ce da aka saba gani a jarirai.
An kiyasta cewa jarirai shida cikin goma na samun cutar, ciki har da bakwaini.
Abin da ke haddasa cutar a cewar hukumar shi ne, jarirai na da jajayen kwayoyin halittar jini masu yawa a jikinsu.
Kuma wadannan kwayoyin halittar suna fashewa, yayin da jikin jariri ke saurin samar da wasu.
Hukumar ta kara da cewa farfashewar da jajayen kwayoyin halittar jinin ke yi ne, ke samar da wani sinadari da ake kira biluribin, wanda shi ne ya ke sauya launin fata da wasu sassan jikin jariri.
Hakan yana faruwa ne saboda a lokacin da aka haifi jariri, halittar hantarsa ba ta kammala giniwa ba, don haka ba ta iya tace wannan sinadari daga cikin jini.
Amma idan jariri ya kai mako biyu da haihuwa, a lokacin ne hantarsa ke iya fara aiki sosai wajen cire wannan sinadari, in ji hukumar.
Sai dai a kan samu wasu lokutan da shawarar kan zamanto wata alama ta wani ciwo.