Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Alamomin cutar sankarar bakin mahaifa da matakan kariya
Latsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton:
Cutar bakin mahaifa tana da alamomi wadanda idan mace ta gani, kuma ta je asibiti a kan lokaci za a iya maganin cutar, a cewar likitoci.
Kimanin mata 14,000 ne ke kamuwa da wannan cuta duk shekara a Najeriya.
Cutar tana da matakai daga na daya zuwa na hudu.
Likitocin cutar sankara sun ce cutar daji ta bakin mahaifa tana da alamun da suka hada da zubar jini da wani ruwa mai wari ko zubar jini bayan saduwa.
Wadannan alamu an fi ganinsu ne a lokacin cutar tana mataki na farko da na biyu.
Likitocin sun kara da cewa idan kuma cutar ta kai mataki na hudu zuwa na biyar, alamomin da mai wannan ciwo za ta gani sun hada da kumburin kafafuwa.
Za ta dinga yawan zubar da jini, kuma zubar ruwa mai warin zai karu.
Haka kuma za ta dinga ciwon kai da ciwon baya.
Maza da mata dai na kamuwa da kwayar cutar HVP mai janyo cutar daji.
Sai dai idan ba a yi magani ba har cutar ta kai gwamman shekaru a jikin mutum, sai ta yi ta ci tana bazuwa.
Ta hanyar yin gwaji a asibiti ne ake gano kwayar cutar da wuri kuma a yi maganinta.