Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Cutar sankara na kama mutane miliyan biyar duk shekara
Latsa hoton sama domin sauraren shirin
Cutar sankara na karuwa a duniya, inda sabbin mutane miliyan biyar ke kamuwa da cutar a duk shekara.
Wata mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar da ke yaki da cutar daji ta kasa da kasa, Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ce ta bayyana haka.
Ta kara da cewa a Najeriya ma cutar tana karuwa.
Dr. Zainab ta ce a kasar, an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar fiye da 123,000 a shekarar 2021.
Haka kuma likitar ta ce cutar sankarar mama ita ce ta fi damun mata a fadin duniya.
Yayin da a kasar Amurka, fiye da mata 13,000 ake ganowa suna dauke da cutar sankarar bakin mahaifar duk shekara.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce a cikin nau'ukan cutar daji da ake fama da su, an fi samun nasarar magance cutar sankarar bakin mahaifa.
Sai dai ta ce hakan ya dogara ne da gano cutar tun da wuri, kuma idan an dauki matakan da suka dace a kan kari.
Inda ta kara da cewa matan da basu da damar samun isa ga cibiyoyin kula da lafiya su suka fi fama da wannan cuta.
Haka kuma yawancinsu suna kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga.
Hukumar ta kuma bayyana muhimmancin tantance mata domin gane ko suna dauke da wannan cuta.
Inda ta bayar da shawarar a yi tantancewa mai nagarta sosai, ga kashi 70 cikin dari na mata masu shekara 35 zuwa 45 a duniya.
Ko da yake daga lokaci zuwa lokaci kuma, ya kamata a tantance dukkan mata manya, domin gano ko suna dauke da sankarar ta bakin mahaifa, in ji hukumar.