...Daga Bakin Mai Ita tare da Kabiru Makaho na Daɗin Kowa

An wallafa

Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 72, shirin ya tattauna da Kabiru Makaho na fim ɗin Daɗin Kowa.

Tauraron fim ɗin ya bayyana cewa shi ɗan asalin Jihar Katsina ne a arewa maso yammacin Najeriya sannan kuma ba makaho ba ne a gaske.

Sunansa na gaskiya Mainasara Abdussalam.

Kazalika ya shaida irin nasarori da ƙalubalan da yake fuskanta a sana'ar tasa.

Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdussalam Usman

Gabatarwa da tsarawa: Halima Umar Saleh