Ra'ayi Riga: A Fada a cika kan bibiyar ayyukan raya mazabu a Kano

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin

A Najeriya, an bayyana rashin bibiya da kuma cikakkiyar doka a matsayin babban tarnaki wajen aiwatar da ayyukan raya mazabu wato constituency project.

A kowacce shekara hukumomi a kasar kan ware makudan kudade domin gudanar da wadannan ayyuka a mazabu daban-daban na fadin kasar, sai dai jama’a da dama na ganin kamar kwalliya bata biyan kudin sabulu.

Kan haka ne BBC Hausa tare da hadin guiwar gidauniyar MacArthur suka shirya wata tattaunawa a birnin Kano kan wannan matsalar.