Lafiya Zinariya: 'Abin da ya sa mace ke jin zafin wankin ciki'

An wallafa

Ana yi wa matan da suka yi bari wankin ciki, domin fitar da ragowar abin da aka rasa. Sai dai ga wadda aka taba yi wa ta san abu ne mai zafi sosai.

Likitoci sun ce wankin mahaifa yana da muhimmanci wajen kare lafiyar mata, musamman ga macen da ta yi bari, ko da dan tayinta ya mutu a ciki, ko kuma wadda mabiyiya ta rage mata a ciki.

Ku latsa hoton da ke sama don sauraroon shirin:

Wata makala da aka wallafa a watan Mayun shekarar 2021, ta bayyana cewa, a fadin duniya ana samun bari kimanin miliyan 23, duk shekara.

Makalar wadda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta ce, bari na janyo matsalar zuban jini ga mata.

Mujallar ta bayyana cewa an fi samun hadarin zubewan ciki a tsakanin matan da ke da karancin shekaru, wato wadanda suka gaza shekara 20 a duniya.

Haka kuma matan da suka haura shekara 35, suma suna fuskantar wannan hadari.

Ta bangaren maza kuma, idan sun haura shekara 40, cikin da suka samar yana cikin hadarin zubewa, in ji makalar.

Wata likitar mata da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Dr. Maryam Suleiman, ta ce babu wani adadi na yawan wankin cikin da za a iya yi wa mace a rayuwa.

Haka kuma a cikin shirin lafiya zinariya na wannan makon ta shaida wa Habiba Adamu dalilin da yasa wankin ciki ya ke da zafi.