Ra'ayi Riga: Yadda zaɓukan APC mai mulkin Najeriya suka gwara kan 'ya'yan jam'iyyar

An wallafa

Latsa hoton sama ku saurari Shirin Ra'ayi Riga:

Shirin ra'ayi Riga na wannan makon ya duba rarrabuwar kai da zaɓukan neman shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a matakin jihohi suka haifar tsakanin 'ya'yanta.

Shirin wanda ke zuwa muku ta rediyo duk ranar Juma'a, ya samu baƙuncin shugaban APC na Jihar Kano da Ɗan Majalisa mai wakiltar Birnin Kano Sha'aban Sharaɗa da sauransu.