Gane Mani Hanya tare da Sanata Ibrahim Shekarau

An wallafa

Latsa hoton da ke sama don sauraren hira da Sanata Ibrahim Shekarau:

Da dama 'yan Najeriya na yi wa majalisar dokokin kasar kallon 'yan amshin-Shatan fadar shugaban kasa.

Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da yadda aka ga bangarorin na aiki tare.

Ana dai ganin an dade ba a samu yanayin da bangarorin biyu suka hade kai ba kamar yanzu duk kuwa da cewa bangarorin kan samu rashin fahimta a wasu batutuwan.

Sanata Ibrahim Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya shaida wa Ibrahim Isa cewa sanya kishin kasa a gaba shi ne dalilin da ya sa bangarorin biyu suke yin aikin tare.