Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Matsalar wutar lantarki a Abuja
Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron shirin:
A Najeriya baya ga matsalar karancin wutar lantarki wadda ta zama jiki ga al’ummar kasar, wata matsala da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya ita ce sau da dama sai mutanen unguwa sun yi karo-karon kudi domin sayen na’urar transfoma, dan ba su da ita ko kuma hada kudin gyara idan ta lalace matukar suna son su ci gaba da samun wutar lantarkin.
A bisa tsari dai wannan nauyi ya rataya ne a wuyan kamfanonin rarraba wutar latarki masu zaman kansu, wadanda gwamnatin tarayyar kasar ta sayar wa bangaren domin ganin yadda za a bunkasa shi.
Hakan na faruwa ne kuwa duk da cewa kayan da al’ummar ke hada kudi su saya yana zama mallakin kamfanin da zarar aka fara amfani da shi.
Haruna Ibrahim Kakangi ya duba wannan matsala, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana daga Abuja.