Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayi Riga: Ce-ce-ku-ce kan faduwar jarrabawar JAMB a Najeriya
An wallafa
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron tattaunawar
A wannan makon shirin Ra'ayi Riga ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya da dama musamman ɗalibai suka yi ta kokawa kan rashin nasarar da suka yi a jarrabawar shiga manyan makarantu ta ƙasar wato JAMB, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.
Shirin ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi don gano wadanne dalilai suka janyo haka kuma me hakan yake nufi ga makomar karatu a jami'oi da sauran manyan makarantu.