Lafiya Zinariya: Dalilan da ke janyo yawan ɓarin ciki

An wallafa

Likitoci sun bayyana cewa mai ciki za ta ga wasu alamomi da ke nuna mata cewa ta yi bari.

Wasu daga cikinsu sun hada da ciwon mara da zuban jini ko fitan gudan halittar mutum ko zuban ruwan da dan tayi ke kwanciya a ciki.