Ra'ayi Riga: Haramta amfani da Twitter a Najeriya

An wallafa

Latsa hoton da ke sama ku saurari shirin Ra'ayi Riga

Ranar Juma'a, 4 ga watan Yuni, gwamnatin Nigeria ta bayar da sanarwar dakatar da shafin sada zumunta na Twitter a kasar.

Wannan lamari ya janyo cecekuce a ciki da wajen kasar. Yayin da wasu na cewa matakin ya saba doka, wasu kuma na cewa gwamnatin ta yi daidai.

Wannan ne batun da muka tattauna a kai a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon, wanda ke zuwa muku duk ranar Juma'a da dare.