Gane Mini Hanya: Ƙaruwar fyaɗe ga ƙananan yara a Najeriya

An wallafa

Ku latsa hoton sama don sauraron shirin:

A Najeriya, har yanzu ana ci gaba da nuna damuwa kan karuwar fyade musamman ga kananan yara.

A baya-bayan nan dai jihohi da dama sun bullo da tsauraran matakai da nufin magance matsalar, koda yake masu fafutika na ganin har yanzu matsalar ta na karuwa.

Wani batu da yanzu haka ke jan hankulan jama’a shi ne na kisan wata karamar yarinya 'yar shekara shida bayan wasu sun yi mata fyade, a garin Marabar Jos da ke jihar Kaduna.

Akan haka ne Mai dakin gwamnan jihar Kaduna Hajiya Aisha Ummi El-Rufai ta ziyarci iyayen yarinyar bayan ta ji rahoton BBC kan lamarin.

Kuma a filin Gane Mani Hanya na wannan makon, Yusuf Tijjani ya tattauna da ita kan matsalar fyaden—farko dai ya fara ne da tambayar ta yadda ta ji kan kisan da aka yiwa karamar yarinyar.