Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Yadda mutanen da Boko Haram ta raba da gidajensu ke cikin mawuyacin hali
Latsa hoton sama domin sauraren shirin
Dubban daruruwan mutane ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, musamman a arewa maso gabashin Najeriya, baya ga ɗaruruwa da suka rasa rayukansu.
Mutanen da suka fito daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa, da dama na neman mafaka ne a sansanonin 'yan gudun hijira a sassa daban-daban na kasar yayin da wasu kuma ke zaune da ‘yan uwa da bokan arziki.
Sai dai kuma galibin 'yan gudun hijirar dake zaune a sansanonin na cikin wani mawuyancin hali na matsin rayuwa musamman a wannan lokaci na azumi da ake sabunta abinci lokacin buda baki.
Zahraddeen Lawan ya ziyarci wani sansanin ‘yan gudun hijira don ganin yadda suke buda baki, ga kuma rahoton da ya hada mana.