Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda 'ya'yana takwas suka mutu a ciki'
Wata mata mai suna Hadiza Mohammed ta bayyawa BBC yadda ta haifi yara takwas dukkaninsu suka mutu a wajen haihuwa.
Ta ce likitoci ba su kai ga gano dalilin da yasa take wabi ba.
'Yadda nake dawainiya da ciki daga karshe kuma dan ya mutu, abin yana sosa mini rai' inj i Hadiza
Matar ta ce duk da cewa ta rungumi kaddara, sai dai fata fitar da rai ba.
Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce akalla ana samun mace daya da ke haihuwar jariri ba rai, a cikin haihuwa 200 da ake samu a kasar Ingila.
Inda ta kara da cewa ba ko da yaushe ake iya kaucewa mutuwar jarirai a ciki ba.
Amma akwai wasu hanyoyin da za a iya bi domin rage hadarin faruwar hakan.
Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da kaucewa wasu daga cikin abubuwan da suke haddasa mace-macen.
Wato mai ciki ta daina shan taba da giya da kuma shan miyagun kwayoyi.
Haka kuma ta dinga zuwa awon ciki, ta kuma kiyaye kamuwa da cututtukan da kan janyo wannan matsala.
Kuma a duk lokacin da ta ji ciwon ciki ko jini na fita ta gabanta ko kuma kaikayi, ta shaida wa ma'aikatan lafiya .
Sannan mai juna biyu ta dinga kula da motsin jaririnta.
Hakazalika, ta dinga kwanciya ta gefenta na dama ko hagu, maimakon kwanciya a rigingine.
Musammam idan ciki ya kai mako 28.
Mai ciki ta dinga cin abinci mai gina jiki tare da kiyaye wasu nau'ukan abinci da ka iya shafar lafiyar jaririnta.