Gane Mini Hanya: Tattaunwa kan matsalolin APC tare da Farouk Adamu Aliyu kan batun Tinubu

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

‘Yan jam’iyyar APC mai mulki sun musanta cewa wani bangaren jam’iyyar na yi wa daya daga cikin jiga-jigan APC na kasa, Bola Ahmed Tinubi kora da hali.

Wani al’amari da ya fito da zaman tankiya a jam’iyyar a baya-bayan nan dai shi ne yadda Bola Tinubu ya fito ya bayyana korafinsa dangane da shirin sabunta rijista da jam’iyyar APC ta gudanar.

A hirarsa da Usman Minjibir, Farouk Adamu Aliyu wanda jigo a jam’iyyar ya ce babu kanshin gaskiya cewa ana son yi wa Bola Tinubu kora da hali daga APC.