Ra'ayi Riga: Cutar kansa da hanyoyin magance ta

An wallafa

Za ku iya latsa hoton sama domin sauraren cikakken shirin

Cutar kansa na daya daga cikin cutuka da ke sanadiyar mutuwar miliyoyin jama'a a duniya, a duk shekara.

Ranar hudu ga watan Fabrairun kowace shekara ce aka kebe a matsayin ranar cutar kansa ko ciwon daji ta duniya.

An kebe ranar ce domin kara fadakar da al'umma game a wannan cuta wadda bincike ya nuna tana sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane a duk shekara a duniya.

Filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon ya tattauna ne game da cutar, da nau'o'inta, da alamominta da kuma matakan da za a iya dauka domin shawo kanta kafin ta gagari magani.

Shirin ya kuma ji irin matakan da gwamnatoci ke dauka na yaki da cutar.