Lafiya Zinariya; hira da likita kan taɓin hankaln da ke samun mutum bayan fuskantar tashin hankali

An wallafa

Sau da yawa, bayan fuskantar tashin hankali kamar hatsari ko gobara ko 'yan fashi ko yaƙi mutum kan shiga wani irin yanayi na firgici da fargaba.

Ƙwararru a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce wannan firgici wani nau'i ne na taɓin hankali wanda aka fi sani da Post Traumatic Stress Disorder ko PTSD.