Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Ciwon sanyi na janyo ciki a bayan mahaifa
An wallafa
Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin, wanda ci gaban na makon da ya gabata ne:
A kasashe masu tasowa kamar Najeriya, ciwon sanyi na daga cikin manyan dalilan da ke janyo wa mata samun ciki a bayan mahaifa.
Haka kuma ana samun asarar rayukan mata masu ciki, saboda jininsu ya tsiyaye a sanadiyyar matsalolin ciki a bayan mahaifa.
Dokta Hauwa Musa Abdullahi ta yi cikakken bayani kan yadda ciwon sanyi ke janyo ciki a bayan mahaifa, da ma wasu dalilan da kuma hanyoyin kauce musu.