Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: ‘Yadda na samu ciki a bayan mahaifa’
An wallafa
Latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:
Matsalar samun ciki a bayan mahaifa na daga cikin abubuwan da ke ci gaba da zama babban kalubale ga likitoci, duk kuwa da ci gaban kimiyya da fasaha da aka samu a duniya.
Don kawo yanzu babu wata hanya ta sauya wa dantayin mazauni, wato a mayar da shi cikin mahaifa domin ya rayu, kuma ita ma uwa ta yi goyon cikin ba tare da wata gagarumar matsala ba.
Ko da yake idan an gano mace na dauke da ciki a wajen mahaifa tun da wurwuri, kuma aka dauki matakan da suka dace, hakan na rage hadarin da za ta iya shiga.