Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Hawan jini na janyo jijjiga ga masu ciki
An wallafa
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:
Ana yi wa cutar hawan jini lakabi da cuta mai kisan mummuke, saboda ba kasafai take nuna alamomi a jikin mutane da dama da ke dauke da ita ba.
Wannan cuta na da hatsarin gaske, musamman ga wasu rukunin mata masu juna biyu, ta yadda har ya kan janyo musu jijjiga.
Haka zalika cuta ce da ke shafar wasu muhimman gabobi na bil’adama, musamman idan ba a gano ta da wuri ba kuma ba a dauki matakan da suka dace ba.
A wannan shiri na Lafiya Zinariya, likita ta yi bayani kan matakan kaucewa cutar da kuma rage tsananinta.