Gane Mani Hanya 29/03/2020

An wallafa

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikaken shirin:

Daidai lokacin da annobar coronavirus ke shafar dumbin mutane da hallaka wasu a fadin duniya, haka kuma cutar ta durkusar da dumbin harkokin rayuwa ciki har da na ilmi.

Hukumomi sun rufe makarantu da jami'o'i, lamarin da ya sanya dalibai komawa gida, suna jiran gawon shanu.

Manyan makarantu da jami'o'i musamman a kasashen da suka ci gaba, tuni suka mayar da harkokin koyarwarsu kan intanet, don haka dalibai na iya ci gaba da karatunsu daga gida.

To amma sauran fa? Mai yiwuwa wannan dalili ne da ya sa wasu kwararru daga Najeriya kaddamar da wani shafin intanet mai suna OpenSchool Nigeria.

Wannan dai tsari ne da wasu masu ba da ilmi da ke da shaidar kwarewa daga Kamfanin Google a Najeriya suka bullo da shi don tallafa wa daliban kasar da malamansu ci gaba da harkokin koyo da koyarwa a wannan lokaci.

Editanmu na Abuja, Yusuf Ibrahim Yakasai ya tuntube su ta wayar tarho, inda suka tattauna kan wannan sabon tsari.