Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Matakan kariya daga Coronavirus ga mata da yara
Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin:
Likitoci sun bayyana wasu hanyoyi da mata za su bi domin kare kansu da sauran iyali, a yayin da annobar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya.
Cutar wadda ta yi ajalin dubban mutane ta bulla a nahiyar Afirka, kuma hakan ya kawar da tunanin da wasu ke yi na cewa cutar ba ta kama bakar fata.
Sai dai da alamu akwai sauran rina a kaba, domin kuwa har yanzu wasu suna tababa kan matakan kariyar da hukumomi ko masana a fannin kiwon lafiya ke bayarwa.
Annobar ta bulla a Afrika a daidai lokacin da nahiyar ke fuskantar kalubale na rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da tsaftataccen ruwan sha ga kuma yawan al’umma.