Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya kan yadda ake safarar jakuna a Najeriya 14/03/2020
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraro:
Jaki dabba ce da ake amfani da ita wajen sufuri da dakon kaya da kuma ayyukan gida da na gona a mafi yawan kasashe masu tasowa, musamman a yankuna na karkara, har ma da wasu birane.
Sai dai a baya-bayan nan, jakunan sun fara fuskantar barazanar gushewa a bayan kasa sakamakon yadda ake cin namansu da kuma amfani da fatarsu wajen samar da wasu magunguna musamman a kasar China.
Wani bincike da wata kungiyar kare jakuna, wadda ke gabashin Afirka mai suna Brooke East Africa ta gudanar, ya nuna cewa a shekara ta 2018 kusan jakuna 16,000 aka sace daga kasashen Afirka 22.
Wannan yasa wasu kasashe da dama a nahiyar, kamar su Uganda da Tanzania da Senegal da Kenya suka hana fataucin jakunan zuwa kasashen waje.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Muhammad Annur Muhammad ya duba barazanar da jakunan ke fuskanta, ga kuma rahoto na musamman din da ya hada mana: