Cin zarafin da ya shafi jinsi: 'Boyayyar annobar' da ta addabi Kenya

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Lokacin da cutar korona ta fada wa Kenya, an samu karuwar cin zarafin da ake yi wa wani jinsin.

Sai dai ba a cika shigar da kara kan batun ba saboda tsoro da kyama da kuma rashin yarda da 'yan sanda.

An bayyana hakan da cewa wata 'boyayyar annoba’ ce da ta addabi kasar Kenya.

Wakilin shirin Africa Eye Tom Odula ya gudanar da bincike kan abubuwan da suke haddasa wannan cin zarafi, inda ya gano yadda lamarin ya yi katutu, sannan 'yan sanda da gwamnati ba sa iya hukunta masu aikata wannan laifi.