Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashiyar da ta zagaye Najeriya dalilin wasan kwallon golf
Wasan kwallon golf, wasa ne da wasu ke yi wa kallon maza ne kadai ke iya yin sa musamman a Najeriya.
Sai dai wata mata mai kamar maza da ta shekara kusan goma tana buga wannan wasa ta ƙware tare da kai wa matakin mai horaswa.
Christine Aboccho, wata matashiya ce da ke zaune a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya.
Matashiyar ta ce sha'awar golf da kuma jajircewa ne ya sa ta kai matakin mai horaswa bayan shiga wasan gadan-gadan.
Da aka tambaye ta irin nasarori da ta samu sakamakon wasan sai ta ce "Gaskiya a cikin shekara 10 da na yi ina buga wannan wasan na gode Allah saboda ya kai ni wurare da yawa kuma ya kai ni kasashe da yawa, a Najeriya kam babu inda ban taba zuwa ba".
Ta kara da cewa tuni ta gina gidan kanta a cikin birnin Fatakwal kuma ta samu aiki sannan ta hadu da mutane da yawa wadanda suka taimake ta a rayuwa.
Matashiyar ta ce ta shiga wasan kuma ta ƙware ne sakamakon ƙwarin gwiwa da take da shi wanda take ganin mata irinta za su iya.
Christine tana da aure kuma mijinta ma mai buga wasan golf ne, amma ta ce ba soyayya ce ta ja ta cikin wasan ba saboda kafin su hadu da mijin da ta aura ma ta jima tana wasan.
"Ba soyayya ce ta ja ni cikin golf ba. Mahaifiyata daga Gombe take kuma lokacin da take da rai tana buga wasan, daga nan ni ma na shiga a ciki muka hadu da shi. Idan kika lura zaki ga mutane da yawa da iyalansu suna buga wannan wasan," in ji Christine.
An tambaye ta yadda take hada zaman aure da kuma wasanni kasancewar akwai tafiye-tafiye da yawa cikinsa, sai ta ce babu wata takura daga wajen mijinta.
"Zaman duniya hakuri ne da kuma yarda, sau da dama ina yin tafiye-tafiye ba tare da mijina ba kuma ya yarda da ni kuma na yarda da shi don haka babu wata matsala".