Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasu mata suka bai wa mazajensu taimakon ƙodarsu
Tia Wimbush da Susan Ellis sun shafe shekaru goma suna aiki tare, kuma duk da cewa ba su san juna ba sosai, shakara biyu da ta gabata sun gano cewa mazajensu na bukatar a yi mu su dashen koda a asibiti.
A watan Agustan bara sai wani abin al'ajabi ya faru.
Matan biyu sun gamu a wani ban daki yayin da su ke bakin aiki, kuma nan take su ka fara hira da juna. Suna da batutuwan da su ka zama iri daya a rayuwarsu, domin dukkansu ma'aikatan sashen da ke kula da na'urori masu kwakwalwa a asibitin kananan yara da ke birnin Atlanta ne, kuma dukkansu na kulawa da matsalolin rashin lafiyar mazajensu a gida.
Kuma kowaccensu gwaji ya tabbatar ba za ta iya ba mai gidanta kodarta guda daya ba domin a dasa ma sa ita, kuma akwai dogon layin masu bukatar dashen kodar wanda ya sa babu wanda ya san ranar da za a zo kansu.
A lokacin ne Wimbush ta tambayi Ellis nau'in jinin mijinta.
Sai Ellis ta sanar da ita cewa yana da nau'in jini mai lamba "O" ne.
Ita kuma Wimbush sai ta sanar da Ellis cewa mijinta na da nau'in jini "AB" ne.
A nan ne fa matan su ka kalli juna cike da mamaki. Nan ta ke su ka gane cewa sun samo mafita ga matsalar da ta dame su - wato za su iya ceto rayukan mazajen nasu a lokaci guda.
Sai Wimbush ta ce lallai akwai yiwuwar za ta iya ba mijin Ellis kodarta daya, domin jinisu iri daya ne, kuma - ta ce Ellis n iya taimaka wa mijinta saboda irin jininsu daya su ma.
Wimbush ta tuna shawarar da su ka yanke, "sai na sanar da Susan cewa ai kuwa akwai babbar dama a gabanmu ta taimaka wa mazajenmu su sami lafiya."
"A nan ne mu ka yanke shawarar yin gwaji."
Jim kadan bayan wannan ganawar, sai gwajin da su ka yi su ka tabbatar cewa jinin ko wace mace ya dace da jinin mijin daya matar.
Saboda haka a watan Maris na bana, wata bakwai ke nan bayan da su ka tattauna batun a ban dakin asibitin da su ke aiki, Wimbush ta ba Lance Ellis mai shekara 41 kodar ta guda, inda ita ma Susan Ellis ta ba Rodney Wimbush mai shekara 45 koda daya.
An yi aikin dashen kodar ne a asibitin Piedmont Atlanta ranar 19 ga watan Maris, kuma dukkan mazajen sun sami waraka - har ta kai ga sun fara fita yawon hawa dutse tare da abokai da 'yan uwansu, inji Tia Wimbush.
Ta kara da cewa kowannesu ya amfana da kyautar da ta sabunta rayuwarsa - abin farin ciki ne ka ga yadda rayuwarsu ta sauya bayan sun shafe shekaru ana tace musu jini a kai a kai.
An yi wa mazajen biyu da matansu biyu fiɗa tare, wato an yi tiyata hudu ke nan, kuma ba a sami wata matsala ba.
Wata uku bayan wannan abin sosa zuciyar, Susan Ellis da Tia Wimbush sun fara magana kan batun, da zummar ba sauran mutane karfin gwuiwar taimaka wa masu bukata wani bangare na jikinsu.