Bidiyon Ku san Malamanku tare da Sheikh Aminu Daurawa

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata aya a Al-Ƙur'ani.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin sabon shirinmu mai taken "Ku San Malamanku".

Ya ce ayar da ta fi ba shi wuya ita ce wata aya da ke cikin Suratul Baqara, wato Iza Tadayantum..., wadda ita ce ayar da ta fi kowace tsawo a littafi mai tsarki.