Ku San Malamanku tare da Dakta Ibrahim Iliyasu

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Dakta Ibrahim Iliyasu, malamin addinin musulunci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

An haifi Malamin ne a shekarar 1973 a unguwar Gama sannan ya taso a Gandun Albasa kuma a can ya yi karatun Firamare daga 1977 zuwa 1984.

Dakta Ibrahim ya yi sakandare ne a makarantu uku, Sharada da KTC da kuma Kawaji daga shekarun 1984 zuwa 1990.

Daga nan sai Mallam ya tafi tilawa da kuma zurfafa ilimin addini na tsawon shekara bakwai.

Ya yi nasarar wakiltar Najeriya a gasar karatun AlKur'ani mai tsarki ta duniya da ta gudana a kasar Masar har sau biyu.

Mallam ya yi karatu a Jam'iar Musulunci da ke Madina a Saudiyya sannan ya yi digiri na uku a Jami'ar Musulunci ta kasa da kasa, International Islamic University da ke kasar Malesiya.

Dakta Ibrahim ya ce abun bakin ciki da ba zai manta da shi ba shi ne rasuwar mahaifiyarsa.

"Mahaifiyata ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a rayuwa ta, domin ita ta fara saya min AlKur'ani bayan haka sai ta yi tafiya aikin Hajji a shekarar 1985 lokacin shekara ta 12 kuma da ni aka raka ta har filin sauka da tashin jirage sai kawai aka ce mana ta bata, aka yi ta nema ba a ganta ba".