Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Salihu Tanko Yakasai: Abin da ya sa nake takarar gwamnan jihar Kano
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Dan takarar kujerar gwamna karkashin jam'iyar PRP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya Salihu Tanko Yakasai ya ce ya tsaya takara ne domin inganta yadda ake gudanar da mulki.
Salihu wanda aka fi sani da Dawisu, ya ce habaka tattalin arziki ne babban abun da zai mayar da hankali kai.
"Za mu mayar da hankali wajen gyara tattalin arzikin Kano, misali idan ka dubi kasuwar 'Yan kaba, ta na bukatar zamanantarwa ta hanyar samar da na'u'rorin sanyi da ake adana kayan abinci".
Baya ga tattalin arziki kuma, yace samar da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da kyautata muhalli su ne sauran abubuwa da zai mayar da hankali kai idan ya samu nasara.
Da aka tambaye shi ko ya tsaya takara ne don raba kuri'un wasu 'yan siyasa sai yace ya tsaya ne don ya ci zabe ba hana wani cin zabe ba.
Kan batun damawa da matasa kuwa, Dawisu yace yana da matasa da yawa da ke goya masa baya ba wai kawai a shafukan sada zumunta ba.
"Ni ba dan siyasar soshiyal midiya ba ne kawai ko kuma na Abuja, muna tare da matasannan kuma duk al'amarinsu da ya tashi da mu ake yi don haka ni na matasa ne" in ji Salihu
Salihu Tanko Yakasai da aka fi sani da Dawisu a shafukan sada zumunta, tsohon mai bada shawara ne kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan Kano na yanzu Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Gandujen ya sauke shi ne daga mukamin a watan Fabrairun 2021 bayan da ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.