Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A kwana uku kacal albashina ke karewa - Ma'aikacin gwamnati a Abuja
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A shekarar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da sabon mafi ƙarancin albashi bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka jajirce.
Duk da ƙarin da aka yi ɗin, ma'aikatan gwamnati a Abuja, waɗanda su ne kusan mafi yawa a babban birnin ƙasar, na koka wa kan yadda albashinsu ba ya kai su ko ina a wata.
Ana sanya Abuja a cikin biranen da suka fi tsadar rayuwa a Njaeriya, musamman kan abin da ya shafi hayar gida kuɗin makarantar yara na boko da Islamiyya da cefane da kuɗin mota da kuɗin asibiti da dai sauransu.
A baya-bayan nan kuma an samu hauhawar farashi sosai a ƙasar, hakan kuma bai sa an ƙara yawan albashin ma'aikata ba.
Mafi ƙarancin albashin ma'aikatan shi ne naira 33,000 a wata, wato ko dala 100 bai kai ba.
A wannan rahoton na musamman, Fatima Othman ta bi wani ma'aikacin gwamnatin tarayyar Najeriya mai suna Mu'azu Ibrahim, bayan da ya karɓi albashinsa a ƙarshen wata, inda ta ga yadda yake kashe kudin.
Malam Mu'azu dai ya ce a mafi yawan lokuta kwana uku kacal albashin ke yi sai ya ƙare.