Ranar Mahaifi ta Duniya: 'Na shiga tashin hankali bayan rasa mahaifina'

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A yayin da ake bikin Ranar Uba ta Duniya a yau Lahadi, 19 ga watan Yuni, wata matashiya Aisha Danjuma Dauda, wacce ta rasa mahaifinta shekara biyu da suka gabata, ta ce rashin mahaifi "musamman idan an shaku da shi ba karamin al'amari ba ne".

A hirarta da BBC Hausa, ta bayyana cewa "Abin da zan fada wa 'yan mata da sauran mutane da mahaifansu ke raye shi ne; su yi amfani da wannan damar don kyautata musu."

Matashiyar ta ce takan tuna yadda mahaifinta yake rarrashin 'ya'yansa idan ya fahimci ya bata musu rai cikin hikima.