Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon yadda aka rushe gidajen Musulmai bayan zanga-zangar adawa da ɓatanci ga Annabi
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Hukumomi a Jihar Uttar Pradesh da ke kasar India sun rushe gidajen Musulmai da dama wadanda suka yi zargin cewa suna da alaka jerin zanga-zangar da aka gudanar kwanakin baya wadanda suka rikide zuwa tarzoma.
An gudanar da jerin zanga-zangar ne bayan wasu jiga-jigan jam'iyyar Bharatiya Janata Party guda biyu sun yi kalaman batanci kan Annabi Muhammad (SAW).