Bidiyon yadda aka ceto yaro dan wata 18 daga rijiya a Indiya

An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Rundunar sojin Indiya ta ceto wani yaro ɗan wata 18 daga wata rijiya mai zurfi a jihar Gujarat da ke yammacin ƙasar.

Yaron mai suna Shivam ya faɗa rijiyar ne mai zurfin mita 90 a bisa tsautsayi.

Wasu sojoji ne suka yi gaggawar zuwa ƙauyen Dudapur da ke kusa da wata cibiyarsu don ceton yaron.

An ciro shi ne ta hanyar amfani da ƙugiyar da aka ɗaure a jikin igiya, sannan aka kai shi asibiti mafi kusa, inda aka sallame shi bayan kwana biyu.