Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Madu Bulamari
An wallafa
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An haifi Malam Muhmmad Abubakar da aka fi dani da suna Madu Bulamari a kauyen nariku a karamar hukumar bama, ranar 1-1-1959.
Kasancewar in da aka haife shi, a kusa da Jamhuriyar Kamaru ne, wanda Kogi ne kadai ya raba su.
Sai aka miƙa shi hannun wani shahararren malami Shahararren malami Goni Madu Yachammaye, amma kafin wannan lokacin sai da ya fara karatu hannun kakansa, da ya kai shekara bakwai zuwa takwas ne aka miƙa shi hannun Gono.