Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Tashin hankalin da labarin ƙarya da aka sa hotona ya jefa ni a ciki'
Dannan hoton sama don kallon bidiyon:
Wannan bidiyon hira ce da BBC ta yi da ɗan jaridar nan na Najeriya Ayodeji Rotinwa, wanda aka yi amfani da hotonsa aka yaɗa labaran ƙarya da aka alaƙanta da wani mai suna Christopher Uche-Ayodeji (Dr Chris) a Facebook, da aka ce ya yi wasu kalamai bayan kisan Deborah Samuel da ake zarginta da zagin Annabi Muhammad a Sokoto.
Ya bayyana yadda ya ga hotonsa na yawo har ya yaɗu kamar ruwan dare a shafukan sada zumunta da kuma tasirin da hakan ya yi na tarwatsa nutsuwarsa.
An ce matashin ya wallafa wani saƙo ne da ke cewa a lokacin yana hidimar ƙasa a arewacin Najeriya a matsayin likita, ya yi ta barin Musulmai suna mutuwa a kan idonsa tare da ƙin taimaka musu, don ramuwa ga wani rikicin addini da ya taɓa shafar danginsa.
Daga baya an gano babu mai wancan sunan nan Christopher Uche-Ayodeji da aka ce ya fadi hakan.