Matashin da ke zane-zane da fasahar 3D

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Abdulmumin Idris, wani matashi ne mai shekara 30, da ke zane-zane masu magana ta tsarin fasahar 3D, inda hotunan ke motsi.

Matashin yakan rubuta wasannin kwaikwayo da zummar fadakar da yara masu tasowa - dangane da tarbiyya da tarihi da kuma yada al'adun Hausawa.

Daya daga cikin manyan labaran da Abdulmumin ya zana ta wannan fasaha ta 3D shi ne fitaccen labarin Magana Jari ce.