Dalilin da ya sa muka kori Sheikh Nuru Khalid daga limaci

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Sanata Sa'idu Muhammad Dansadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisar Najeriya na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.

Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.

A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin.

Wasiƙar ta ce: "Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi'ar mutum.