Bidiyon yadda Osinbajo ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa a Kaduna

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar jaje tashar jirgin ƙasa a Kaduna.

Ya kuma ziyarci asibitin sojoji ta 44 domin ganin mutanen da suka jikkata a harin da ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja a ranar Litinin.