Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Adamu Girbo Muhammad

An wallafa

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daMalam Girbo:

An haifi Malam Adamu Girbo Muhammad a birnin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 27 ga watan Disambar 1951.

Ya yi karatun allo a birnin na Gombe a wurin malamai da dama da suka hada da Malam Usman da Malam Manu da Wazirin Ciroman Gombe da sauransu.

Bayan ya kammala karatun Alkur'ani mai girma, Malam Girbo ya yi karatun litattafai a karkashin manyan Malamai irin su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya da Malam Balarabe.

A shekarar 1968, malamin ya tafi Kaduna inda ya shiga sojan Najeriya domin fafatawa a Yakin Basasa.

"Da na shiga soja a garin Kaduna ina da sana'a a lokacin don na samu lasisi na tuka mota a 1967; da lasisin ya shekara daya na tafi Lagos inda a kan hanya ne na tsaya a Kaduna na shiga soja. Daga nan aka debe mu aka kai mu Enugu a jirgin kasa," in ji malamin.

Ya kara da cewa da suka isa Enugu ne aka tambayi wadanda suka iya aikin kafinta ko tuki da wasu sana'o'i inda ya bayyana cewa shi direba ne, yana mai cewa daga nan ne aka dauke su aka koma da su Kaduna inda ya rika tuka tirela.

Malam Girob ya ce yayin zamansa a Kaduna ne ya hadu da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya "kuma su ne suka kwadaita mini karatu."

"Kasancewa aikinmu yana zuwa ne lokaci zuwa lokaci, sai ya zamana ina da dama na yi rika karatu irin na zaure, shi ya sa na je a gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi," a cewar malamin.

Ya kara da cewa bayan babban malamin ya fahimci irin basirar ne ya samar masa gurbi a Kwalejin Koyar da Larabci da Addinin Musulunci da ke Katsina sannan ya sa aka mayar da shi fannin limamai daga bangaren direbobi.

Malamin ya ce ya kammala karatunsa na shekara hudu ne a daidai lokacin da ake shirin kafa kungiyar Izala, kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa ta.