Aisha Ibrahim Galadima: Matashiyar Injiniya da ta gina wasu manyan gidaje a Abuja

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo:

Wata matashiya da ta karanci aikin injiniyan gine-gine ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda yadda gine-gine suke birge ta.

Aisha Ibrahim Galadima ta shaida wa BBC cewa a matsayinta na injiniyar gine-gine ta taka rawa sosai wajen gina wasu manya-manyan gidaje a Abuja.

A cewarta "abin da ya sa na karanci harkar injiniyarin shi ne ina ganin gidaje a waje, ina mamaki yadda aka gina shi ya zauna ba tare da wata kishingidewa ba. Abin na burge ni sai na ce ni ma bari na ga yadda ake gina gida tun daga farko har karshe."

Matashiyar, 'yar asalin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta ce wani saurayinta ya guje ta saboda ita injiniya ce tana mai cewa ba ta ga dalilin da zai sa ta fasa wannan sana'a ba tun da kusan kowacce sana'a ko aiki akwai mace da namiji da ke yinsu.

Wasu bidiyoyi da za ku so ku kalla: