Bayanin Kwamishinan Addinai na Kano kan wa'azin Daurawa na al'aurar mata

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi wa Malaman addinin Musulunci gargadi da masu amfani da shafukan sada zumunta da su lura da abin da suke faɗa domin harshe ka iya kai su ya baro su.

Kwamishinan addinai na jihar Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ya bayyana matsayar gwamnatin Jihar Kano kan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke bayan yaɗuwar wani bidiyo da Sheikh Daurawa ke magana a kan al'aurar mata da kuma martanin da Nafisa Ishak wata mai amfani da shafin Tiktok ta yi.

Ku aklli bidiyon don jin cikakken bayanin Baba Impossible.