Abba Gandu: Mutumin da ya shekara 50 yana kula da zakuna a Kano

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wani mutum da ke kula da namun daji a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana irin dadin da yake ji wajen gudanar da ayyukansu.

Malam Abba Gandu ya shaida wa BBC Hausa cewa ya soma aikin kula da namun daji ne tun 1971.

Ya kara da cewa a duk shekarun da ya kwashe yana kula da namun dadi, babu wata dabba da ta taba cizonsa.