Bidiyon Ku san Malamanku tare da Albanin Gombe, Ustaz Adam Muhammad Murtadha

An wallafa

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daUstaz Adam Muhammad Murtadha:

An haife shi a karamar hukumar Ajingi da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya a shekarar 1978.

Malamin ya soma karatunsa na allo a wurin mahaifinsa, Malama Murtala, wanda shi ma malamin addinin Musulunci ne.

Daga bisani ya koma Unguwar Bachirawa da ke cikin birnin Kano, inda ya yi karatu a wurin wani fitaccen Malami mai suna Malam Garba.

Ustaz Adam ya kara da cewa bayan rasuwar mahaifinsa ya tafi Gombe wurin kakansa mai suna Malam Abdulhamid wanda aka fi sani da Malam Karami inda ya ci gaba da karatun Alkur'ani.

"Baya da Allah ya ba ni ikon samun karatun Alkur'ani, sai kuma na shiga makarantar gaba da firamare mai suna Government Arabic College, Gombe, inda na kammala ta a 2007.Daga nan kuma na ci gaba da karatu a wurin Malamai, sanna kuma na yi Diploma a fannin Larabci," a cewarsa.