Bidiyon yadda kotu ta tura Danbilki Kwamanda kurkuku

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari.

Danbilki zai gaba da zama a gidan yari har zuwa 15 ga watan Maris.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.

Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.