Yakin Ukraine: Dubban masu goyon bayan Rasha sun yi zanga-zanga a Belgrade

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Kimanin mutum 4,000 sun shiga zanga-zangar goyon bayan Rasha a babban birnin kasar Serbia.

Zanga-zangar da aka gudanar tana nuna goyon baya ga Moscow bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.

Serbia tana da dangantaka ta addini da kabila da kuma siyasa da Rasha ta shekaru aru-aru.