Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Umma Shehu: Duk aikin zunuban da nake yi, ba na yin shirka
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Fitacciyar tauraruwar finafina-finan Kannywood ta ce ta bar masu zaginta da Allah domin kuwa shi ne zai saka mata.
Ta bayyana haka ne a hira da BBC Hausa domin yin raddi ga masu zaginta bisa zargin tana aikata ba daidai ba.
Ta ce a matsayinta na Musulma, tana yi wa Allah laifi kuma ta san zai gafarta mata amma duk da irin laifukan da take yi masa "ba na yin shirka."
Tauraruwar ta ce ya kamata masu ganin ta aikata ba daidai ba su rika jan hankalinta ba kawai su rika zaginta ba.
A cewarta masu zaginta na kallo za ta shiga aljannah ta bar su suna dakon zunuban da suka dauka saboda zaginta,