Wannan shi ne bayani a kan shugaban Ukraine Zelensky

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Lokacin da Volodymyr Zelensky ya fara bayyana a talabijin a matsayin shugaban kasar Ukraine, ya yi haka ne a matsayin dan fim cikin wani shirin talabijin na barkwanci mai farin jini.

Sai dai mafarkinsa ya zama gaskiya a watan Afrilun 2019 bayan da ya zama shugaban kasar a zahiri.

A yanzu yana jagorantar kasar mai mutum miliyan 44 wadda ke fuskantar hare-hare daga Rasha.

A wasan talabijin mai suna Servant of the People (Bawan Jama'a), Zelensky ya taka rawar wani malamin tarihi a makaranta wanda ya zama shugaban kasa bayan da wani bidiyonsa ya bayyana a intanet yana kalamai masu zafi kan cin hanci da rashawa.

Bidiyon ya ja hankulan 'yan Ukraine, wadanda sun gaji da kwamacalar 'yan siyasar kasar.