Yan Ukraine mazauna Birtaniya na shirin komawa Kasarsu don yin yaki

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wasu ƴan Ukraine da dama da ke zaune a Birtaniya sun yi ta sayen kayan yaƙi a shirin da suke yi na komawa ƙasarsu domin shiga filin daga.

BBC ta yi magana da wasu ƴan Ukraine da za su yi tafiyar kilomita 2,000 a mota don kafiya da kayan yaƙin da suke buƙata.

Sun sayi hulunan kwano da rigunan sulke da kayan kare lafiya daga kamfanoni masu zaman kansu a Landan.