Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon zamantakewar mata da mijin da suke zaune a gari daban-daban
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 31 ɗin, shirin ya yi duba ne kan yadda mata da mijin da suke zaune a gari daban-daban za su kyautata zamansu.
Watakila da yawanmu da yake zaune muke da iyalanmu a waje guda, ire-irena, ba mu cika tunanin yaya zamantakewar ma'auratan da kaddarorin rayuwa suka tunkuda su zama a wurare daban-daban ba.
Amma akwai miliyoyin ma'auratan da ke cikin irin wannan yanayin. Misali, mata na Najeriya miji na China, ko kuma mata na Giade a Bauchi, miji yana Abuja.
Dalilai da dama ka iya sa hakan kasancewa kamar yadda mutane biyun da na tattauan da su a shirin na yau Sayyada Rahama Abdulmajid da Sheikh Jabir Maihula suka shaida min.
Kar kuma fa ku ce wai a bisa son rai rayuwar ta kasance musu a haka, a'a ƙaddarorinsu ne suka zo a hakan, ku ma muma ba mu san yaya kaddarar za ta rikide mana ba watarana, kamar yadda Hausawa ke cewa wai ba haka aka so ba, ƙanen miji ya fi miji kyau.
Kuma ma ba ku san wani abu ba, wasu na ganin an fi ɗokin juna idan aka dan yi nesa da junan, ana taren nan an fi yawan fada, don haka a nan wasu lokutan ma'auratan da ba sa taren ma sun fi mu morewa, don kullum sai musayar kalaman i miss you, da ilove you ake aikawa.